Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Beckham ya buga wasansa na farko a yayin da Paris Saint Germain ta lallasa Marseille da ci 2-0

Tsohon Kyaftin tin kasar Ingila, David Beckham ya buga wasansa na farko a sabuwar club dinsa ta Paris Saint Germain tun bayan dan wasan ya saka hanu a kwantiraki da PSG bayan ya baro LA Galaxy, inda PSG ta lallasa abokiyar hamayyarta Marseille da ci 2-0. Beckham wanda a da ya taba bugawa Manchester United da Real Madrid wasa, ya shiga wasan ne minti na 76, kuma shi ya taimaka aka zira kwallo ta biyu a ragar Marseille.  

David Beckham a lokacin da ya fara bugawa PSG wasanta da Marseille, PSG ta samu nasara da ci 2-0
David Beckham a lokacin da ya fara bugawa PSG wasanta da Marseille, PSG ta samu nasara da ci 2-0 REUTERS/Charles Platiau
Talla

Beckham a yanzu haka shine dan wasa dake da mafi yawan shekaru a gasar ta French League inda a yanzu haka yake da shekaru 37.

A yanzu haka PSG ta bawa Lyon tazarar maki uku a teburin gasar ta French Ligue.

A sauran wasannin da aka buga, Bordeaux ta sha mamaya a gidanta a hanun Brest da ci 2-0 itama, sannan Lyon ta doke Lorient da ci 3-1.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.