Isa ga babban shafi
Champions League

Juventus ta lallasa Celtic 3-0, PSG ta doke Valencia 2-1, Madrid za ta kece raini da United

Juventus ta lallasa Celtic ci 3-0 a gasar Zakarun Turai, haka kuma PSG ta doke Valencia a gidanta ci 2-1. Sai dai a karawar su ta biyu PSG za ta buga wasan ne ba tare Zlatan Ibrahimovic saboda dan wasan ya karbi jan kati. A yau Laraba ne Duniya za ta kwashi kallo a wasa tsakanin Real Madrid da Manchester United.

Tambarin kungiyar Real Madrid da Manchester United wadanda za su kece raini da juna a gasar Zakarun Turai.
Tambarin kungiyar Real Madrid da Manchester United wadanda za su kece raini da juna a gasar Zakarun Turai. Cristianoronaldofan.net
Talla

Manchester United za ta sabunta adawar da ke tsakaninta da Real Madrid inda tagawar Mourinho za su karbi bakuncin tagawar Farguson a wasan da Duniya ke jira. Tun a shekarar 2003 da Real Madrid ta sha da kyar ci 6-5 a zagayen Kwata Fainal kungiyoyin biyu ba su sake haduwa ba.

“Wannan wasa ne da Duniya ta ke jiran ganin yadda zai kaya” inji Mourinho.

Akwai tsohuwar adawa da ke tsakanin Mourinho da Ferguson, tun Mourinho yana FC Porto a Portugal da kuma lokacin da ya ke horar da ‘Yan wasan The Blues na Chelsea.

A karshen mako Mourinho ya je sa ido a Filin wasan Old Trafford inda Manchester United ta doke Everton ci 2-0.

Farguson yace karawa ce ta fitar da gwani tsakanin manyan kungiyoyin Turai guda biyu.

A ranar Talata, Juventus ta lallasa Celtic ci 3-0 a gasar Zakarun Turai, haka kuma PSG ta doke Valencia a gidanta ci 2-1. Sai dai a karawar su ta biyu PSG zata buga wasan ne ba tare Zlatan Ibrahimovic saboda dan wasan ya karbi jan kati.

Ana minti uku da fara wasa ne kuma Juventus ta samu zira kwallo a ragar Celtic bayan dan wasan Najeriya Efe Ambrose da ya lashe kofin Afrika ya yi kuskure, wanda ya ba Alessandro Matri damar zira kwallon a raga.

Bayan dawowa hutun rabin lokaci ne Juventus ta sake zirara wasu kwallayen biyu a ragar Celtic.

‘Yan kasar Argentina ne guda biyu Ezequiel Lavezzi da Javier suka zirawa PSG kwallayenta a ragar Valencia kafin mintinan karshe Adil Rami ya zirawa Valencia kwallo a ragar PSG.

A yau Laraba akwai wasa tsakanin Shakhtar Donetsk da Borussia Dortmund.

Sai a ranar 20 ga watan Fabrairu ne AC Milan za ta fara karbar bakuncin Barcelona a San Siro, bayan Arsenal ta kara da Bayern Munich a ranar 19 ga watan Fabrairu.

Kungiyar Galatasaray ta Turkiya da ta yo cefanen Didier Drogba da Wesley Sneijder za ta karbi bakuncin Schalke 04 a ranar 20 ga wata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.