Isa ga babban shafi
India

Matukin motar da aka yiwa wata daliba fyade a India ya rataye kansa a gidan yari

Matukin motar da akawa wata daliba fyade a kasar India wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar ta daga baya, ya kashe kansa a dakin gidan yarin da yake tsare,a yayin da ‘Yan uwansa ke ikrarin kashe shi aka yi. Ram Singh ya kasance daya daga cikin mutane shida da ake zargi a bisa aikata wannan aika-aika, an kuma same shine a mace kamin wayewar gari, inda ‘Yan Sanda suka bayyana cewa Singh ya rataye kansa ne a gidan yarin Tihal, dake birnin Delhi.  

Motar dake dauke da wadanda ake zargi da yin fyade ga wata daliba, akan hanyarsu ta zuwa gidan yari
Motar dake dauke da wadanda ake zargi da yin fyade ga wata daliba, akan hanyarsu ta zuwa gidan yari REUTERS/Stringer
Talla

“Ya yi amfani da kayan jikinsa ne, inda ya hadasu ya daura sannan ya rataye kansa a rufin dakin bayan ya taka wata kujerar katako.” Inji wani Jami’in gidan yarin.

Sai dai mahaifin yarinyar da akwa fyade, wadda ‘yar shekaru 23 ce, ya bayyana cewa akwai sakaci a bangaren jami’an dake tsaron gidan yarin.

“Mun kasa gane ko menene ya sa ‘Yan sanda suka kasa kare shi, sun san cewa shi ne mutumin da aka fi zargi a wannan aika-aika da akawa ‘ya ta.”

Mahaifiyar Singh ta ce ta kadu matuka bayan da ta sami labarin mutuwar dan ta.

A watan Disambar bara ne aka wa dalibar fyade aka kuma mata duka tare da saurayinta a cikin wata mota kirar Bas, inda kuma ta rasu a ran 29 ga watan Disambar bayan an yi fafutukar ceto ranta a wani asibiti dake Singapore.

Fyaden, wanda ya jawo bore a sassa daban daban na kasar ta India ya haskaka kasar a matsayin kasa da bata mayar da hankali wajen kare hakkin mata ba, ganin yadda ake samun yawaitar yiwa mata fyade.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.