Isa ga babban shafi
Faransa

Dakarun Faransa sun hallaka ‘Yan tawaye 15 a Mali

Kasar Faransa ta ce dakarun ta sun hallaka ‘Yan tawayen kasar Mali 15 a daren jiya, sakamakon musayar wutar da suka yi a tsakanin su. Ministan tsaron Faransa, Jean Yves Le Drian ne ya sanar da kashe ‘Yan tawayen, inda yake cewa sojojin su sun yi nasarar kashe wasu daga cikin ‘Yan tawayen da dama a cikin ‘yan kawanakin nan. 

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande REUTERS/Alexander Nemenov/Pool
Talla

Ministan ya ce dakurun nasu sun kai harin dare ne a sansanin ‘yan tawayen dake tsaunin Ametettai, inda suka kashe 15 daga cikin su.

Dakarun kasar Faransa sun kaddamar da hare hare ne a tsakiyar watan Janairu, dan ceto kasa daga hannun ‘yan tawayen da suka karbe Yankin Arewacin ta, na kusan shekara guda.

Harin dai ya yi nasarar korar ‘yan tawayen daga garuruwan da suka kama, inda suka tsere zuwa tsaunukan kasar, suka kaddamar da hare hare.

Ya zuwa yanzu, kasashen Afrika da dama, sun tura sojojin su dan kakkabe ‘yan tawayen, yayin da Amurka da Jamus suka tura nasu sojojin dan horar da sojojin Mali.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.