Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta ce an sake kashe mata soja guda a Mali

Kasar Faransa ta ce an sake kashe mata soja guda a kasar Mali, sakamakon fafatawar da suke cigaba da yi da ‘Yan tawayen kasar, wanda yanzu haka ya shiga mako na bakwai. Kakakin sojin Faransa, Kanar Thierry Burkhard, ya ce an kashe Kofur Cedric Charenton ne a tsaunin Adrar des Ifoghas dake iyakar Algeria, yayin da su kuma suka kashe ‘Yan Tawayen 15. 

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande REUTERS/Alexander Nemenov/Pool
Talla

A wani banagren kuma, MinistanTsaron kasar Faransa, Jean-Yves Le Drian, ya nemi da a yi taka tsantsan yayin da ake ikrarin cewa an kashe Mokthar Belmokhtar, mutumin da ake zargi da kista harin da aka kai wata ma’aikatar tace iskar gas a Algeria.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.