Isa ga babban shafi
Amnesty-MDD-Sudan

Amnesty tace MDD ta gaza a yankin Abyei

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Amnesty International, ta zargi dakarun samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da gazawa wajen kare mutanen Abyei, daga harin sojin Sudan da kuma ‘Yan Tawaye, abinda ya sa mutane sama da 100,000 suka gujewa gidajensu.

Gobarar wuta a gidajen mazauna Yankin Abyei a kasar Sudan.
Gobarar wuta a gidajen mazauna Yankin Abyei a kasar Sudan.
Talla

Daraktan kungiyar, Donatella Rovera, yace shigar dakarun a Yankin, ya nuna sojin da ‘Yan tawaye sun kori daukacin mutanen da ke garin na Abyei, da kuma kona musu gidaje.

Tuni kakakin sojin Sudan, Swarmi Khaled Saad ya yi watsi da zargin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.