Isa ga babban shafi
GASAR TURAI

Za a kai ruwa rana tsakanin PSG da Barcelona a Paris

Duniya – Yau ake kai ruwa rana tsakanin kungiyar PSG ta Faransa da Barcelona ta Spain a wasan kwata final na cin kofin zakarun Turai.

Kylian Mbappé na PSG
Kylian Mbappé na PSG © AFP - FRANCK FIFE
Talla

Hukumomin kasar Faransa sun sanar da daukar tsatsauran matakan tsaro domin kare lafiyar 'yan kallo da kuma 'yan wasan kungiyoyin biyu dangane da duk wata barazanar tsaron da ka iya tasowa.

Kungiyar PSG na ci gaba da samun tagomashi sosai a wasannin ta duk da raba hannun rigar da tayi da fitattun 'yan wasa irin su Lionel Messi da Neymer Jnr, kuma yanzu haka ta kama hanyar lashe gasar Ligue 1.

Kylian Mbappé da Frenkie De Jong a karawar da suka yi a shekarar 2021
Kylian Mbappé da Frenkie De Jong a karawar da suka yi a shekarar 2021 © AFP / FRANCK FIFE

A bangare daya Barcelona na 'dan fama da matsaloli a wasannin ta na cikin gida, ganin yadda Real Madrid ta bata tazara a gasar La Liga.

Saboda haka masu sharhi a kan harkokin wasanni ke kallon wannan karawar a matsayin mai matukar muhimmanci a gare ta, yayin da ita kuma kungiyar PSG ke neman ganin ta lashe wannan kofi a karon farko, saboda irin makudan kudaden da ake kashe mata.

Wannan ne karo na farko da Barcelona ke zuwa wannan mataki a cikin shekaru 4 da suka gabata, duk da sanin cewar sau 5 tana lashe wannan gasar.

Wani abin lura shi ne yadda masu horar da 'yan wasan wadannan kungiyoyi 2 Luis Enrique da Xavi Hernandez suka fito daga kungiya guda ta Barcelona, inda suka yi wasa, kana suka jagorance ta.

A shekarar 2015, Enrique ya lashe kofuna 3 wa kungiyar Barcelona, kafin daga bi sani ya rabu da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.