Isa ga babban shafi
Gasar Zakarun Turai

PSV da Borussia Dortmund sun buga kunnen doki a zagayen kungiyoyi 16

Kwallon da Luuk de Jong ya saka a raga daga bugun daga kai sai mai tsaron raga ce ta bai wa PSV Eindhoven damar buga canjarar 1 da 1 da Dortmund a Zubin farko na matakin zagayen kungiyoyi 16 a gasar zakarun nahiyar Turai.

'Yan wasan PSV  a yayin murnar kwallon da De Jong ya ci a wasansu da Dortmund.
'Yan wasan PSV a yayin murnar kwallon da De Jong ya ci a wasansu da Dortmund. AFP
Talla

Dan wasan gaban na Netherlansds ya farke kwallon da Dortmund ta saka musu ne a cikin minti 10 da dawowa hutun rabbin lokaci, bayan da alkalin wasa ya yanke hukunci cewa Mats Hummels ya rafke Malik Tillman a cikin da’ira ta 18.

Donyell Malen ne ya ci wa Dortmund kwallo kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Za a buga zubi na biyu na wannan wasa a ranar 13 ga watan Maris.

PSV ce ta fi samun damammakin saka kwallaye a raga a wasan kafin a tafi hutun rabin lokaci amma ta gaza saka ko da guda a raga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.