Zakarun Turai: City za ta buga da Copenhagen, Arsenal da Porto
Mai rike da kofin zakarun nahiyar Turai, Manchester City za ta fafata da Copenhagen a matakin kungiyoyi 16 a gasar, a yayin da Arsenal ta barje gumi da FC Porto ta kasar Portugal.
Wallafawa ranar:
Copenhagen ta kasar Denmark, wadda ta lashe gasar kasar, ta kai wannaan matsayi ne a karon farko tun bayan shekarar 2011.
Za a buga Zubin farko na wannan gasa ne a ranakun 13 da 14 da 20 da 21 ga watan Fabrairun shekarar 2024, kana a yi zubi na biyu a ranakun 12 da 13 ga watan Maris.
City da Arsenal duk za su buga wasanninsu na farko ne a gida.
Real Madrid, wadda sau 14 ta lashe wannan kofi na zakarun nahiyar Turai za ta fafata da RB Leipzig, a yayin da Inter Milan, wadda ta kammala gasar shekarar da ta gabata a matsayi na biyu za ta buga da Atletico Marid, a yayin da Bayern Munich za ta kara da Lazio.
Za a yi wasan karshe na wannan gasa ne a filin wasa na Wembley a Ingila, a ranar 1 ga watan Yuni.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu