Isa ga babban shafi

Kane ya ci kwallaye 20 a wasanni 14 da ya buga a gasar Bundesligar Jamus

Harry Kane ya ci kwallonsa ta 20 daga wasanni 14 a gasar Bundesligar Jamus a wasan da Bayern Munich ta doke Stuttgart a ranar Lahadi, wasan da ya ci kwallaye biyu a cikinsa.

Harry Kane, dan wasan gaba na Bayern Munich.
Harry Kane, dan wasan gaba na Bayern Munich. REUTERS - WOLFGANG RATTAY
Talla

Kane, dan kasar Ingila, wanda yake wasansa na 14, ya saka kwallon da Leroy Sane ya kawo masa a cikin dakikoki 90 da fara wasa.

Bayan da alkalin wasa ya soke kwallayen da Thomas Muller da Kim Min-jae suka saka  raga saboda sun yi satar fage, kane ya saka kwallo ta biyu.

Kim Min -Jae ya ci wa Bayern kwallo ta uku da kai, kuma kwallo ta farko kenan da ya ci wa Bayern Munich tun da ya fara mata wasa.

Kane ya ci kwallaye 20 a cikin wasanni 14 da ya buga, kuma da haka ya waragza tarihin da tsohon dan wasan Hamburg Uwe Sealer, wanda ya ci kwallaye 20 daga wasanni 21 a kakar Bundesliga ta 1963-64, sai kuma dan wasan City Haaland, wanda ya ci kwallaye 20 daga wasanni 22 a lokacin da ya ke Borussia Dortmund.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.