PSV Eindhoven daga Netherland, ta doke Lens a gasar zakarun Turai
A gasar cin kofin zakarun Turai, a karo na farko kungiyar kwallon kafar Lens ta kasar Faransa ta yi kasa a gwiwa yayin fafatawa da kungiyar PSV Eindhoven daga kasar Netherland, wacce ta doke Lens da ci 1 da nema.Dan wasan kungiyar PSV Eindhoven Luuk de Jong mai shekaru 33 ne zura kwallo a ragar ta Lens vayan mituna 12.
Wallafawa ranar:
Baya ga wannan wasa,mu sanar da masu sauraren mu cewa Real Madrid,Real Sociedad,Inter Milan,Bayern Munich sun samu tikitin su na kasancewa a mataki na gaba a wanan gasar cin kofin zakarun Turai.
A rukunin farko ko rukunin A.
Fc Copenhague ta doke Manchesterd United da ci 4 da 3,yayinda Bayern Munich ta doke Galatasaray da ci 2 da 1.
Ranar 29 ga wannan watan da muke cikin sa Galatasarai da Manchesterd United za su haduwa.
A rukuni Ba, Arsenal ta doke Sevilla da ci 2 da nema,kuma kamar dai yada aka ji PSV Heidhoven ta doke Lens da ci 1 mai ban haushi.
A rukunnin na uku ko rukunnin C Naples daga Italia ta yi kunen doki da Union Berlin daga Jamus 1 da 1.
Sporting Braga ba ta ji da dadi ba bayan karawa da Real Madrid,wacce ta doke ta da ci 3 da nema.
A rukunni Da ko rukuni na hudum,Real Sociedad ta doke Benfica da ci 3 da 1.Sai Inter Milan da ta lalasa Salzbourg da ci 1 mai ban haushi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu