Isa ga babban shafi
Gasar Zakarun Turai

Arnautovic ya taimaka wa Inter wajen doke Atletico a zagayen kungiyoyi 16

Marko Arnautovic, wanda ya shiga wasa daga baya ya ci wata kwallon da ta bai wa Inter Milan nasara a kan Atletico Madrid a zubi na farko na matakin kungiyoyi 16 a gasar zakarun nahiyar Turai a daren Talata.

Marko Arnautovic na Inter bayan ya ci Atletico Madrid.
Marko Arnautovic na Inter bayan ya ci Atletico Madrid. AP - Luca Bruno
Talla

Mai tsaron ragar Atletico, Jan Oblak ya ture wata kwallon da Lautaro Martinez ya buga mai, amma sai ta fada kafar dan wasan gaban na Austria, shi kuma ya narka mai ita a raga da karfin tsiya.

Arnautovic ya baras da damammakin saka kwallo a wasan tun da farko kafin wannan dama ta samu.

Tsohon dan wasan gaban na West Ham, Arnautovic ya maye gurbin Marcus Thuram ne, wanda ya samu rauni kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Alvaro Morata ya shigo wasan bayan hutun rabin lokaci amma ya gaza yin katabus a wasan da shi ne na 100 da kocin Atletico, Diego Simeone ya jagoranta a gasar Zakarun nahiyar Turai.

Atletico za ta karbi bakuncin zubi na biyu na wannan wasa a filinta na Civitas Metropolitano a ranar 13 ga watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.