Isa ga babban shafi

Inter Milan ta kawo karshen kwantiragin Alexis Sanchez

Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta kawo karshen kwantiragin dan wasanta na gaba Alexis Sanchez bayan cimma jituwa tsakanin bangarorin biyu.

Alexis Sanchez a kwallon da ya zura yayin wasan Inter Milan da Brescia.
Alexis Sanchez a kwallon da ya zura yayin wasan Inter Milan da Brescia. AFP
Talla

Sanchez dan kasar Chile ya ci kwallaye 20 a wasanni 109 da ya buga wa Inter, wadda ke doka gasar Serie A ta Italiya tun bayan da ya koma kungiyar daga Manchester United  a shgekarar 2019.

Dan wasan mai shekaru 33 ya taimaka wa Inter din wajen lashe kofin Serie a karon farko cikin shekaru 11 a kakar 2020-2021, amma kuma duk da haka da kyar yake samun damar buga wasa kullayaumin.

Ana danganta Sanchez, wanda ya shafe kakar wasa 4 a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta arewacin Landan da komawa Marseille ta Faransa.

Inter  zata yi wasan farko na gasar Serie A na wanna kaka a ranar Asabar da Lecce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.