Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Ban yi nadamar taka leda a Man United ba- Sanchez

Dan wasan gaba Alexis Sanchez ya ce ko kadan bai yi nadamar kulla kwantiragi da Manchester United ba, sai dai kawai bai samu cikakken lokacin taka leda yadda ya kamata ba.

Alexis Sanchez lokacin taka ledarsa a Manchester United
Alexis Sanchez lokacin taka ledarsa a Manchester United Reuters/Carl Recine
Talla

Sanchez dan kasar Chile mai shekaru 30 wanda ya koma Inter Milan a matsayin aro cikin watan jiya bayan shafe watanni 19 a Old Trafford, shi ne dan wasa mafi daukar albashi a United inda ya ke karbar yuro dubu dari 4 kowanne mako amma kuma kwallaye 5 cal ya iya zurawa a wasanni 45 da ya dokawa United din tun bayan sayo shi daga Arsenal cikin watan Janairun 2018.

A cewar Sanchez dalilin da ya baro shi da Arsenal zuwa United a wancan lokaci bai wuce ganin ya lashe kofuna gasa daba-daban ba, amma sai ya rasa samun abin da ya yi tsammani.

Tun bayan da Arsenal da sayo Sanchez daga Barcelona kan yuro miliyan 30 a shekarar 2014, ya zura mata kwallaye 80 cikin wasanni 166 kafin sayar da shi a 2018.

Sai dai sauya shekar dan wasan ana ganin ta haddasa masa koma baya, ko da dai yayi rawar gani a bangaren kasarsa yayinw asannin Copa America da suka gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.