Isa ga babban shafi

Inter Milan ta yi nasarar kaiwa wasan karshe a gasar zakarun Turai

Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta samu nasarar ka iwa wasan karshe na cin kofin zakarun Turai karon farko cikin shekaru 13, bayan doke takwarar ta AC Milan a wasansu na jiya talata da kwallo 1 da nema.

Tawagar Inter Milan bayan nasara kan AC Milan da ya basu damar kaiwa wasan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai.
Tawagar Inter Milan bayan nasara kan AC Milan da ya basu damar kaiwa wasan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai. © Luca Bruno/AP
Talla

Tun a haduwar farko dama an tashi wasa ne 2 da nema tsakanin manyan kungiyoyin Italiyar biyu, wanda ke nuna a jumlace Inter ta yi a nasara a dukkanin wasan da kwallaye 3 da nema.

Zagayen farko na wasan da kuma haduwar ta jiya dukkaninsu sun gudana ne a filin wasa na San Siro, karawar da ta tabbatar da mafarkin Inter na kaiwa wasan karshe na gasar.

A daren yau ne Inter za ta san abokiyar karawarta a wasan na karshe wato bayan wasan Real Madrid da Mancity ko da ya ke mataimakin shugaban kungiyar ta Inter Milan Javier Zanetti ya ce za su yi fatan kaucewa haduwa da Real Madrid a wasan na karshe da zai gudana a birnin Istanbul.

Zanetti wanda tsohon kyaftin din tawagar ta Inter Milan ne ya ce baya fatan haduwarsu da Madrid wadda ta lashe kofin sau 14 a tarihi.

Inter dai ta bayar da mamaki a wannan kaka lura da yadda ta kammala matakin rukuni a matsayin ta biyu kasan Bayern Munich duk kuwa da yadda rukunin ke kunshe da Barcelona inda daga bisani tawagar ta birnin Milan ta kuma doke Porto da Benfica tare da fitar da su daga gasar.

Akwai dai masu ganin abu ne me wuya Inter ta iya kwatar kanta walau a hannun Real Madrid ko Manchester City yayin wasan na karshe a Istanbul.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.