Chelsea ta haye wasan kusa da karshe na kofin Carabao
Chelsea ta yi nasarar zuwa wasan kusa da na karshe na kofin Carabao bayan doke Newcastle 4-2 a bugun fanariti, bayan da aka tashi wasa 1-1 da yammaci Talata.
Wallafawa ranar:
Newcastle ta ja ragamar wasan da kwallon da ta ci tun a mintuna 16 da soma wasa ta hannun dan wasanta Callum Wilson, ana daf da Karkare wasa ne a mintuna na 90 ne Mykhailo Mudryk ya ramawa Chelsea aka tashi wasa 1-1, akaje bugun finareti Blues din ta yi nasara.
Mai tsaron ragar Chelsea Djordje Petrovic ya ceci kungiyar wajen tare bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Kungiyar ta Mauricio Pochettino za ta hadu da Fulham wacce ta doke Everton a bugun fenariti.
Yayin da Middles-brough da ta samu nasara a kan Port Vale da ci 3-0 za ta jira wadda za ta yi nasara a wasan da za’a fafata yau tsakanin Liverpool da West Ham United.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu