Isa ga babban shafi

Za a dauki shekaru 2 kafin martabar Chelsea ta dawo - Pochettino

Kocin Chelsea, Mauricio Pochettino, ya ce za a dauki shekaru biyu kafin kungiyar tasa ta kai matsayin karsashin da ake bukata.

Mai horas da kungiyar Chelsea Mauricio Pochettino.
Mai horas da kungiyar Chelsea Mauricio Pochettino. Action Images via Reuters - MATTHEW CHILDS
Talla

Ya zuwa yanzu a kakar wasa ta bana, wasa guda daga cikin shida Chelsea ta samu nasarar lashewa a gasar Firimiya.

Nasarar ta farko kuwa ita ce wadda kungiyar da ake yi wa taken ‘The Blues’ ta samu kan Fulham da kwallaye 2-0 a ranar Litinin.

Tarihi dai ya nuna wannan shi ne bude farkon kakar wasa mafi muni cikin shekaru 45 da Chelsea ta gani, lamarin da ka iya zama barazana ga sabon kocin kungiyar Mauricio Pochettino watanni kalilan bayan karbar ragamar horas da ‘yan wasan Kulob din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.