Isa ga babban shafi

Hukumar kwallon kafa ta Brazil za ta shigar da kara kan wariyar launin fata

Hukumar kula da kwallon kafa ta Brazil (CBF) ta sanar a ranar Juma'a cewa za ta shigar da kara kan wadanda suka rubuta sakonnin wariyar launin fata a intanet da suka yi wa shugabanta da 'yan wasan kasar hari bayan sun sha kashi a hannun Argentina ranar Talata (1-0).

Magoya bayan kungiyar kwallon kafar Brazil
Magoya bayan kungiyar kwallon kafar Brazil AP - Eraldo Peres
Talla

Hukumar za ta dauki matakan shari'a a kan wadanda ke da hannu a wadannan hare-haren a kan 'yan wasa, magoya baya da kuma Ednaldo Rodrigues shugaban  kungiyar.

Tuni dan wasan gaba na Real Madrid Rodrygo ya yi Allah wadai da hare-haren wariyar launin fata a shafukan sada zumunta a yau Alhamis, kuma ya samu goyon bayan wasu taurarin Brazil, irin su Neymar da Vinicius.

Fernando Diniz, mai horar da kungiyar kwallon kafar Brazil
Fernando Diniz, mai horar da kungiyar kwallon kafar Brazil © Martin Mejia/AP

Hare-haren da hukumar ta Brazil ta yi Allah wadai da su, sun kwatanta 'yan kasar Brazil da birai, kuma kai tsaye aka kaiwa Ednaldo Rodrigues, bakar fata na farko shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar da ta lashe gasar sau biyar a duniya.

A Brazil, wariyar launin fata laifi ne da za a iya yanke hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari.

Lokacin da Rodrygo ke musayaryawu da dan wassan Argentina, Messi, a wasan neman gurbin gasar cin kofin duniya kenan.
Lokacin da Rodrygo ke musayaryawu da dan wassan Argentina, Messi, a wasan neman gurbin gasar cin kofin duniya kenan. REUTERS - RICARDO MORAES

'Yan sanda sun shiga tsakani da karfi don dakile wannan fada tsakanin magoya bayan kasashen biyu, wadanda suka tsinci kansu a matsayi daya sakamakon rashin kebantaccen filin ajiye motoci ga masu ziyara.

A gasar cin kofin duniya na 'yan kasa da shekaru 17 da ke gudana a Indonesia, Argentina ta fitar da Brazil da ci 3-0 a wasan daf da na kusa da na karshe ranar Juma'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.