Isa ga babban shafi

Ina ci gaba da karbar sakonnin zagi tun bayan sa'insarmu da Messi - Rodrygo

Dan wasan gaban Brazil, Rodrygo, ya nuna rashin jin dadinsa, bisa irin kalaman nuna kyama ko kuma zagi da yake gani a shafukansa na sada zumunta, tun bayan sa’insar da suka yi da dan wasan Argentina, Lionel Messi, kafin wasan su da suka buga na neman gurbin gasar cin kofin duniya.

Lokacin da Rodrygo ke musayaryawu da dan wassan Argentina, Messi, a wasan neman gurbin gasar cin kofin duniya kenan.
Lokacin da Rodrygo ke musayaryawu da dan wassan Argentina, Messi, a wasan neman gurbin gasar cin kofin duniya kenan. REUTERS - RICARDO MORAES
Talla

Brazil dai ta yi rashin nasara a wasan da ci daya mai ban haushi a hannun Argentina, a Rio de Janeiro, karo na uku kenan a jere da kasar, wadda ta taba lashe wannan gasa har sal biyar a tarihi, tana samun rashin nasara.

Wasan dai ya samu tsaikon kusan rabin sa’a guda, sakamakon arangamar da ta auku tsakanin ‘yan kallo da jami’an ‘yan sanda, a filin wasa na Maracana.

Messi wanda ya zargi ‘yaan sanda da cin zarafi, an gano shi yana magana da kyaftin din Brazil Marquinhos, a gefe guda kuma an gano yadda yake musayar yawu da Rodrygo, wanda ya ce ya samu sakonnin hoton biri da ayaba a shafukansa na sada zumunta.

“Masu iya sarrafa kalaman nuna kyama na gudanar da aikinsu. Kafofin sada zumuntana, na ci gaba da karbar sakonnin zagi,” in ji Rodrygo a shafinsa na Instagram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.