Brazil ta cire Antony daga cikin tawagarta saboda zargin cin zarafi
Kasar Brazil ta jingine dan wasan gaban Manchester United Antony sakamakon zargin cin zarafin tsohuwar budurwarsa.
Wallafawa ranar:
Hukumar kwallon kafa ta Brazil ta ce an cire dan wasan mai shekaru 23 daga cikin tawagar bayan da aka tabbatar mata cewar ana binciken sa.
'Yan sanda a Sao Paulo da Greater Manchester na gudanar da bincike kan zarge-zargen, wanda dan wasan ya musanta.
Ana zargin Antony da cin zarafin tsohuwar budurwar sa Gabriela Cavallin a wani dakin otal na Manchester a ranar 15 ga watan Janairu, daga bisani ya barta da rauni a ka, wadda har sai da ta kaita ga ganin likita.
Ta kuma yi ikirarin cewa dan wasan ya nausheta a kirji, wanda hakan ya yi sanadin lalacewar dashen mama da silicone da aka mata, kuma likitoci sun tabbatar mata da cewa sai an mata aiki a wurin.
Antony ya jaddada cewa a tarayyarsa da tsohuwar budurwar tasa bai taba cin zarafinta ba.
Zargin ya zo ne bayan da kungiyar ta Premier ta sanar a watan da ya gabata cewa dan wasan gaba Mason Greenwood zai suya sheka ta hanyar yarjejeniya bayan wani bincike na cikin gida na watanni shida da yake fuskanta.
A makon jiya ne dan wasan ya tafi zaman aro kungiyar Getafe ta kasar Spaniya.
Dan wasan gaba na Arsenal, Gabriel Jesus ne ya maye gurbin Antony a cikin tawagar Brazil a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za su kara da Bolivia da Peru.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu