Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Corinthians ta doke Al Ahly a gasar zakarun Duniya

Kungiyar Corinthians ta Brazil ta tsallake zuwa buga wasan karshe a gasar Duniya ta kungiyoyin kwallon kafa bayan doke Kungiyar Al Ahly ta Masar ci 1-0 a wasan kusa da karshe da aka gudanar a kasar Japan.

'yan wasan Kungiyar Corinthians ta Brazil  suna sallama da filin wasa bayan sun doke Ahly ta Masar a Japan
'yan wasan Kungiyar Corinthians ta Brazil suna sallama da filin wasa bayan sun doke Ahly ta Masar a Japan Reuters
Talla

A yau Alhamis ne dai kungiyar Chelsea daga Nahiyar Turai zata kara da kungiyar Montera ta kasar Mexico. Kuma cikinsu duk kungiyar da ta samu nasara ita ce zata kara da Corinthians a wasan karshe.

Ana dai gudanar da gasar ne tsakanin kungiyoyin da suka lashe kofin gasar zakaru a Nahiyoyinsu, kuma duk kasar da ta lashe gasar ita ce zakara a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.