Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Zambia da Brazil sun ce Messi bai kafa Tarihi ba

Hukumar kwallon kafar kasar Zambia da kungiyar Flamengo ta kasar Brazil sun ce za su mika kokensu ga hukumar FIFA da ke kula da kwallon kafa a Duniya domin kalubalantar tarihin zira kwallo a raga da aka ce Messi ya kafa bayan zira kwallaye 88 a bana.

Dan kasar Argentina Lionel Messi da ke taka kwallo a kungiyar Barcelona
Dan kasar Argentina Lionel Messi da ke taka kwallo a kungiyar Barcelona REUTERS/Marcelo del Pozo
Talla

Hukumar Zambia tace akwai dan wasan kungiyar Kabwa Warriors, Godfrey Chitalu wanda ya zira wa kungiyar kwallaye 107 a raga a shekarar 1972. Wanda hakan kuma ya karyata tarihin da aka ce Messi ya kafa.

Chitalu tsohon dan wasan kasar Zambia ne kuma ya taba zama kocin kasar kafin mutuwar shi a shekarar 1993 a hadarin jirgin da ya kashe ‘yan wasan Zambia a Gabon.

A daya bangaren kuma mahukuntan kungiyar Flamengo a Brazil sun ce Zico ya zira kwallaye 89 a shekarar 1989.

A karshen mako ne Lionel Messi ya zira kwallaye biyu a ragar Real Betis wanda ya ba shi damar shan gaban Gerd Mueller wanda ya zira kwallaye 85 a raga a kakar wasa.

Hukumar kwallon Zambia tace zata kalubalanci Messi a gaban hukumar FIFA.

Kakakin Hukumar Zambia yace suna da kundin tarihinsu amma babu shi a kudin tarihin kwallon duniya don haka za su mika koken su ga hukumar FIFA.

A jiya Laraba Lionel Messi ya sake zira wasu kwallaye biyu a raga wanda ya taimaka wa Barcelona lallasa Cordoba ci 2-0 a gasar Copa Del Ray.

Yanzu haka dai Messi yana da jimillar kwallaye 88 a bana, tazarar kwallaye uku ke nan yaba Mueller.

Real Madrid kuma Abokiyar hammayar Barcelona ta sha kashi ne a hannun Celta Vigo ci 2-1. Cristiano Ronaldo shi ne ya fara bude kwallo a raga ana minti hudu da fara wasa. Daga bisani ne kuma Karim Benzema ya fice a fili bayan ya samu rauni a idon kafar shi ana minti 31.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.