Isa ga babban shafi

Wolves ta kawo karshen jerin nasarorin Manchester City a Firimiyar Ingila

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta sha kaye a hannun Wolves da kwallaye 2 da 1, wanda ke kawo karshe jerin nasarorin da kungiyar ke ci gaba da yi tun bayan faro kakar wasa ta bana.

Wolves ta kawo karshen jerin nasarar da Manchester City ke yi a dukkanin wasanninta na wannan kaka.
Wolves ta kawo karshen jerin nasarar da Manchester City ke yi a dukkanin wasanninta na wannan kaka. REUTERS - HANNAH MCKAY
Talla

Nasarar Wolves mai cike da al’ajabi ta zo ne a dai dai lokacin da Manajan City Pep Guardiola ke kallon wasan daga cikin ‘yan kallo sakamakon haramcin wasa guda da ya ke fuskanta.

Tun farko Ruben Dias ne ya zura kwallo bisa kuskure a ragar kungiyarsa Manchester United tun a minti na 13 da faro wasa, ko da ya ke Julian Alvarez ya farke kwallon a minti na 58 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci amma kuma Hwang Hee-chan ya kara wata kwallon a minti na 66.

Tauraron Manchester City Erling Haaland ya rasa dama a wasan na yau ta yadda masu tsaron bayan Wolves suka kange tare da hana shi sakat.

Haduwar ta yau dai ta zama tashin hankali ga Matheus Nunes wanda City ta saya daga Wolves, lura da yadda ya yi rashin nasara a haduwarsa ta farko da tsohuwar kungiyar tashi.

An dai dambarwar da ta kai ga Nunes ya kauracewa atisaye gabanin amincewa da cinikin na shi zuwa Etihad kan farashin fam miliyan 53.

Phil Foden da Jack Grealish sun yi kokari matuka wajen ganin sun sauya nasarar ta Wolves amma kuma masu tsaron bayanta suka kange su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.