Isa ga babban shafi

Luton ta yi nasara karon farko a gasar Firimiya tun bayan kakar wasa ta 1992

Luton ta yi nasarar farko tun bayan fara doka wasannin Firimiyar Ingila da ta dawo a wannan kaka, inda ta doke Everton da kwallaye 2 da 1 har Goodison Park a yau Asabar, kungiyar da ke dawowa gasar mafi girma a Ingila bayan shekaru 32.

Rabon kungiyar da haskawa a gasar firimiya tun shekarar 1992.
Rabon kungiyar da haskawa a gasar firimiya tun shekarar 1992. © AFP - GLYN KIRK
Talla

Everton wadda yanzu ta koma karkashin ikon kamfanin 777, an yi tunanin farfadowarta tun bayan sayar da ita, lura da yadda ta yi nasara kan kungiyoyin Brentford da Aston Villa a jere amma kuma ta wayi gari da shank aye a hannun Luton wadda ke matsayin sabuwa a gasar ta Firimiyar Ingila.

Tun farko ‘yan wasan Luton wato Tom Lockyer da Carlton Morris ne suka zura kwallo ko da ya ke Dominic Calvert-Lewin ya farke guda, amma har aka tashi wasa Everton ba ta iya kara wata kwallo ba.

Wannan nasara dai ita ce makamanciyarta ta farko da Luton ke yi wadda rabonta da ganin irinta tun lokacin da ta doke Aston Villa da kwallaye 2 da nema a gasar ta Firimiya cikin watan Aprilun shekarar 1992.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.