Isa ga babban shafi

Manchester United ta sake shan duka a hannun Crystal Place da kwallo 1 da nema

Manchester United ta sake cin karo da rashin nasara a haduwarta da Crystal Place yau Asabar inda suka tashi wasa kwallo 1 mai ban haushi duk da yadda aka yi tunanin farfadowar tawagar ta Erik ten Hag.

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Erik Ten Hag.
Manajan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Erik Ten Hag. AFP
Talla

Shan kayen na Manchester United na zuwa ne kwanaki 4 bayan ta doke Crystal Palace a wasannin cin kofin kalubale ko kuma Carabao, kuma rashin nasarar na matsayin karo 4 cikin wasanni 7 da tawagar ta doka daga faro wannan kaka zuwa yanzu.

Da farko dai anyi tsammanin United ta dore da nasara lura da bajintar da ta nuna a wasannin Carabao amma sai Palace ta dauki fansar waccan rashin nasara.

An dai tashi wasan ba tare da tawagar ta ten Hag ta iya zura kwallo ba duk kuwa da matsa kaimin da suka yi a zagaye na biyu wato bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Erik ten Hag ya faro wasan da zaratan ‘yan wasansa nag aba 3 da suka kunshi Bruno Fernandes da Rasmus Hojlund da kuma Mason Mount a zagaye na biyu amma duk da haka aka gaza samun sauyi.

Suka dai ta fara tsananta ga tem Hag ganin yadda ya fara kakar wasan ta bana cike da rashin nasara musamman a wasannin firimiya ko da ya ke sun yi nasarar doke Wolves da Nottingham Forest amma kuma suka sha duka hannun Brighton da kuma yanzu a hannun Crystal Palace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.