Isa ga babban shafi

Najeriya ta zo ta 3 a gasar cin kofin kwallon kwando na Afrika bangaren Mata

Najeriya ta kammala gasar cin kofin kwallon kwando ta mata a matsayin ta 3 bayan doke Angola da ci 28 da 24 yayin wasan da suka doka a jiya asabar.

Tawagar 'yan wasan kwallon kwandon Najeriya bangaren mata.
Tawagar 'yan wasan kwallon kwandon Najeriya bangaren mata. Getty Images - Nikola Krstic/MB Media
Talla

Tawagar ta Najeriya ta yi wannan nasara yayin wasan neman gurbin na 3 da ya gudana a Monastir tsakanin tawagar kasashen biyu da kowaccensu ta yi rashin nasara a wasan gab da na karshe.

Tun farko Najeriya ta sha duka ne a hannun tawagar kwallon kwandon Masar wadda ta doke ta da kwallaye 32 da 18 a bangare guda kuma Angola ta sha kaye a hannun Guinea.

Haduwar ta jiya tsakanin Angola da Najeriya a gasar wadda Tunisia ke karbar bakonci tun farko ‘yammatan na Najeriyar sun ratatawa Angola kwallaye 12 ne da 7, yayinda a zagaye na biyu aka kamala wasa 28 da 24.

Masar ta ci gaba da rike kambunta, bayan lashe gasar tac in kofin kwallon kwando na kasashen Afrika, inda ta doke abokiyar karawarta Guinea da kwallaye 29 da 16.

Kocin tawagar ta Najeriya, Shittu Agboola ya yaba da kokarin da ‘yan wasan suka yi wajen iya samun mataki na 3 a gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.