Isa ga babban shafi

Napoli na bukatar Yuro miliyan 500 don sakin Osimhen ya koma Saudiya

Shugaban kungiyar kwallon kafar Napoli Aurelio De Laurentiis ya shaida wa kulob din Al-Hilal na Saudiyya cewa zai iya karban Yuro miliyan 500 ne kawai don sallama dan wasan gaba na Najeriya Victor Osimhen.

Dan wasan Napoli da Najeriya Victor Osimhen
Dan wasan Napoli da Najeriya Victor Osimhen AP - Fabio Ferrari
Talla

De Laurentiis wanda ke cikin shugabannin kungiyiyon kwallon kafar Turai dake neman watsi da tayin Saudiyya mai tsoka, ya na shagube ne ga Al-Hilal a matsayin martini kan bukatar klub din na dauko Osimhen.

Manyan kungiyoyin Turai sun amince da bukatun kungiyoyin Saudiyya daban-daban a wannan bazarar, inda suka sayi fitattun ‘yan wasa kamar Gabri Veiga da Riyadh Mahrez tare da fitar da 'yan wasan su da suka gaji da su kamar Edouard Mendy da Franck Kessie.

Wasu manyan ‘yan wasan Turai sun ki amincewa da tayin Saudi a wannan bazarar ciki har da Lionel Messi da Kylian Mbappe, wanda hakan ya suka fara zawarcin Victor Osimhen, inda Al-Hilal ta yi wa Napoli tayin Yuro miliyan 200 amma ta ki amincewa.

Rahotanni suka ce tayin Yuro miliyan 40 na Al-Hilal a duk shekara ya ja hankalin Osimhen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.