Isa ga babban shafi

Osimhen ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afrika

Dan wasan Najeriya da ke haskawa tare da kungiyar Napoli a gasar Seria A Victor Osimhen, ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka ta bana, yayin karrama ‘yan wasa da ya gudana a birnin Accra na gasar Ghana.

Dan wasan gaba na tawagar Najeriya kwallon kafar Victor Osimhen.
Dan wasan gaba na tawagar Najeriya kwallon kafar Victor Osimhen. REUTERS - JENNIFER LORENZINI
Talla

Kafin lashe kyautar, Osimhen ya yi takara ne da takwarorinsa da ke gasar Firimiyar Ingila Muhammad Salah da kuma Riyad Maharez mai rike da kyautar ta Gwarzon dan kwallon Afirka, wadda ya lashe ta har sau uku a jere.

A kakar wasan da ta kare dai, Osimhen mai shekaru 24 ya ci kwallaye 31, wadanda suka taimaka wa kungiyarsa ta Napoli lashe kofin gasar Seria-A karo na farko cikin shekaru 33.

Dan wasan ya kuma kafa tarihin zama dan nahiyar Afirka da ke kan gaba wajen cin kwallaye mafiya yawa a gasar  Seria A da adadin kwallayen 26, kambin da a baya tsohon gwarzon dan kwallon kafa na duniya George Weah ne ke rike da shi a babbar gasar kwallon kafar ta kasar Italiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.