Isa ga babban shafi

Napoli ta yi wa Osimhen tayin sama da naira biliyan 6 duk shekara

Zakarar gasar Seria A a kakar da ta gabata Napoli, ta yi wa dan wasan gabatanta Victor Osimhen tayin kwantiragin shekaru biyu, inda za ta rinka biyan shi Yuro miliyan 6 da dubu dari biyar kwatankwacin naira biliyan 6 da miliyan dari 5 a duk shekara.

Dan wasan Napoli dan Najeriya Victor Osimhen.
Dan wasan Napoli dan Najeriya Victor Osimhen. REUTERS - JENNIFER LORENZINI
Talla

Dan wasan da ke da ragowar kwantaragin shekaru biyu da kungiyar, ya bukaci ta rinka biyanshi Yuro miliyan 7 a duk shekara.

Osimehen mai shekaru 24 ya taimakawa Napoli wajen lashe gasar Seria A karon farko a cikin shekaru 33, inda ya zura kwallaye 26 a cikin wasanni 32 da ya yi mata a kakar da ta gabata, lamarin da ya sa manya kungiyoyi a Turai ke ta zawarcinsa.

Toh sai dai mai horas da kungiyar Rudi Garcia ya tabbatar da cewar, Osimhen ba zai bar kungiyar a kakar da za’a fara ba.

A gobe Laraba ne ake saran dan wasan na Najeriya ya koma atisayi ta re da sauran ‘yan wasan kungiyar, a shirye-shiryen tun karar kakar da ake dab da farawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.