Isa ga babban shafi

Tennis: Venus Williams ta yi gagarumar nasara karon farko cikin shekaru 4

Shahararriyar ‘yar wasan kwallon tennis, ‘yar kasar Amurka,  Venus Williams mai shekaru 43 ta samu gagarumar nasara  a karon farko cikin shekaru 4, bayan da ta  doke ‘yar kasar Rasha, Veronika Kudermetova a gasar Cincinnati Open.

Venus Williams ta yi gagarumar nasara karon farko cikin shekaru 4.
Venus Williams ta yi gagarumar nasara karon farko cikin shekaru 4. REUTERS - ANDREW COULDRIDGE
Talla

Williams,  ta taso daga baya, bayan an mata  duka har sau biyu, inda ta yi nasara   6-4 7-5 Kudermetova, waddda ke lamba ta 16 a cikin jerin manyan ‘yan wasan tennis na mata a duniya.

‘Yar wasan ta kasar Amurka, wadda sau 7 tana lashe manyan kofunan gasar tennis ta yi ta murmushi a yayin da take murnar wannan nasarar, a gasar da ake yi a cikin kasarta.

Williams, wadda ke lamba  ta 533 a duniya ta  bayyana cewa ta shiga cikin mawuyacin hali sakamakon rauni, amma yanzu tana sa ran samun ci gaba.

Za ta  fafata a wasanta na gaba da ‘yar kasar China, Qinwen Zheng ko ‘yar Belarus Aliaksandra Sasnovich a zagaye na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.