Isa ga babban shafi

Tennis: Tsohuwar lamba daya za ta koma wasa a US Open bayan murabus

Tsohuwar lamba daya a wasan kwallon tennis, Caroline Wozniacki za ta dawo fagen wasa shekaru 3 bayan ta yi ritaya, kuma ta yi amannar cewa za ta iya lashen kofin gasar US Open.

Caroline Wozniacki.
Caroline Wozniacki. REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

‘Yar kasar Denmark din ta lashe gasar Australian Open a shekarar 2018 daga cikin manyan kofuna 30 da ta ci, kuma ta shafe makonni 71 a matsayin lamba daya.

Wozniacki mai shekaru 32 ta yi murabus ne a watan Janairun shekarar 2020 bayan da ta haifi ‘yan tagwayenta.

A wata ganawa da manema labarai, Wozniacki ta ce tana da muradin fafatawa a gasar Canadian Open wadda zai gudana a birnin Montreal a watan Agusta, kafin ta yi balaguro zuwa gasar US Open, wadda ta taba kai wa matakin wasan karshe a shekarun 2009 da 2014.

Za ta kuma kuma fafata a gasarAustralian Open da kuma gasar wasannin Olympic da za ta gudana a birnin Paris a shekarar 2024.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.