Isa ga babban shafi

Tawagar Sweden ta sake gayyatar Zlatan Ibrahimovic

Tawagar Sweden, ta kira Zlatan Ibrahimovic mai shekaru 41 don buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai, shekara guda bayan wasansa na karshe.

Zlatan Ibrahimovic.
Zlatan Ibrahimovic. AP - Alvaro Barrientos
Talla

A karshen wannan watan ne Sweden za ta kara da Belgium da Azerbaijan.

Dan wasan gaban na AC Milan ya yi jinya tsawon kakar wasa ta bana saboda rauni a gwiwarsa.

Zlatan ya ajiye takalmansa bayan gasar Euro ta 2016 amma ya dawo a 2021 don taimakawa kasar samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya, amma hakarsa bata cimma ruwa a wancan lokacin.

Boss Janne Andersson ya ce baya ganin Ibrahimovic "a matsayin wanda ake fara wasa da shi" amma yasan za a yi amfani da shi wajen maye gurbin wasu ‘yan wasan.

Ibrahimovic, wanda ya kasance a benci har sau uku a wasannin da AC Milan ta buga a kakar wasa ta bana, ya buga wa kasarsa wasa a karawar da suka yi da Poland a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a shekarar 2022.

Tsohon dan wasan Manchester United da Paris St-Germain shi ne dan wasan da ya fi zura kwallaye a tarihin kasar Sweden, inda ya zura kwallaye 62 a wasanni 121 da ya buga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.