Zlatan ya yi nasarar zura kwallaye 300 a manyan Lig din Turai
Zlatan Ibrahimovic ya zama dan wasa na 3 a baya-bayan nan da ya kafa tarihin zura kwallaye 300 a wasannin gasar Lig din turai guda 5, bayan kwallonsa ta karshen mako da ta bai wa AC Milan nasarar yin canjaras da Udinese karkashin gasar Serie A.
Wallafawa ranar:
Kwallon ta Zlatan dan Sweden mai shekaru 40, ta bashi damar shiga sahun Ronaldo da Messi da ke da makamantan yawan kwallayen a Turai.
A jumulla dai zuwa yanzu Zlatan na da kwallaye 404 ne da ya zura a tsawon lokacin taka ledarsa ciki har da 16 lokacin taka ledarsa da Malmo wato kungiyarsa ta cikin gida can a Sweden, sai kwallaye 35 lokacin zamansa a Ajax sai 53 karkashin gasar MLS a kungiyarsa ta LA Galaxy.
Zlatan wanda ya taka leda a kungiyoyin AC Milan da Inter Milan da Juventus da PSG da Manchester United da kuma Barcelona kwallayen 300 na matsayin wadanda ya zura karkashin gasar Serie A ta Italiya da Laligar Spain da kuma Firimiyar Ingila baya ga Bundesliga ta Jamus da Ligue 1 ta Faransa.
Sai dai duk da wannan gagarumar nasara, har yanzu Zlatan na kasa da Ronaldo na Manchester United wanda ke da kwallaye 483 a lig din na Turai 5 haka zalika kasa da Messi mai kwallaye 475.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu