Isa ga babban shafi
Wasanni

Zlatan Ibrahimovic ya koma tawagar kwallon kafar Sweden bayan shekaru 5

Zlatan Ibrahimovic ya nuna halin  da ba a saba gani ba, inda har sai da ya zub da hawaye a daren jiya Litinin, bayan da ya koma wasa a  tawagar kwallon kafar kasarsa, Sweden bayan kusan shekaru 5 da barinta.

Dan wasan gaba na AC Milan da Sweden Zlatan Ibrahimovic.
Dan wasan gaba na AC Milan da Sweden Zlatan Ibrahimovic. AFP/Archives
Talla

A wani taron manema labarai, dan wasan bai nuna hali irin na fankama da takama da ya saba nunawa ba.

Da yake ganawa da manema labarai gabanin wasan neman tikitin fafatawa a gasar neman shiga gasar cin kofin Turai ta Euro 2022, Zlatan mai shekaru 39 ya nuna hali na dattaku da hakuri, akasin yadda ya yi a lokacin da ya sanar da yin hannun riga da tawagar kasarsa bayan gasar Euro 2016.

Shahararren dan wasan na kasar Sweden  da AC Milan ya yi murabus daga yi wa kasarsa wasa ne  bayan ya buga wasanni 116 ya kuma jefa kwallaye 62 a raga.

A makon da ya gabata ne dai dan wasan ya bayyana aniyarsa ta yi wa tawagar kasarsa kome ta shafinsa na Instagram.

Ibrahimovic ya ce ba ya so a ba shi dama a tawagar saboda bajintar da ya nuna a baya, sai dai don namijin kokarin da ya ke yi a yanzu.

 Yanzu haka dan wasan gaban yana kan ganiyarsa a kungiyarsa ta AC Milan, inda a gasar Serie A ta Italiya ya ci kwallaye 15 a wannan kaka, ciki har da kwallon da ya ci a ranar Lahadi a wasan da suka lallasa Fiorentina 3-2.

 Ya ce bai damu da sake kasancewa kyaftin din tawagar Sweden  a yanzu ba, mukamin da a halin da ake ciki dan wasa Alexander Granqvist ke rike da shi.

Wata alama kuma da ke nuni da cewa dan wasan ya zama mai saukin kai, Ibrahimovic ya  bukaci a  ba shi riga mai lamba 11, a maimakon lamba 10 da ya saba sanyawa, inda ya ce ya roki dan wasan gaba na Real Sociedad Alexander Isak, kuma  cikin ladabi ya amince.

Sai dai Ibrahmovic bai bar wajen wannan ganawa ba sai da ya ce babu wani dan wasa irinsa a duniya, sai dai a wannan karo, cikin raha.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.