Isa ga babban shafi
Wasanni

Zlatan Ibrahimovic zai samu sauki-Mino Raiola

Wakilin dan wasan Man Utd Zlatan Ibrahimovic, ya ce an yi nasara a tiyatar da aka yi wa dan wasan a cinyarsa. kuma za ta dawo daidai har ya samu daman koma taka leda.

Zlatan Ibrahimovic da Masoyansa
Zlatan Ibrahimovic da Masoyansa REUTERS/Jason Lee
Talla

Dan wasan mai shekaru 35 ya samun mumunar rauni a fafatawar da sukayi da Andelecht a gasar Europa League ranar 20 ga watan Afrilu

Zlatan da ya kusa kawo karshen kwantiraginsa a Old Trafford bai yanke shawarar ko zai sabunta yarjejeniyarsa ba.

Zlatan Ibrahimovic ya zura kwallaye 28 tun bayan dawowarsa United daga Paris St -German a karshen kakar da ta gabata.

Wakilin Zlatan, Mino Raiola, dai ya jaddada cewa ciwon dan kasar ta Sweden ba abu ne da zai yi barazana ga aikinshi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.