Isa ga babban shafi
UEFA-Zlatan

UEFA ta fara binciken Zlatan kan zargin hannun jari a kamfanin caca

Hukumar UEFA za ta ci gaba da bincike kan dan wasan gaba na AC Milan Zlatan Ibrahimovic kan bayanan da ke nuna kawancensa da wani katafaren kamfanin caca da kuma gagarumin hannun jarin da ya ke da shi a kamfanin.

Zlatan Ibrahimovic, dan wasan kungiyar AC Milan dake gasar Seria A a Italiya.
Zlatan Ibrahimovic, dan wasan kungiyar AC Milan dake gasar Seria A a Italiya. AP - Antonio Calanni
Talla

Zlatan dan Sweden, wasu bayanai da jaridun kasarsa suka wallafa ne suka bankado zargin yayinda Uefa ta sha alwashin gudanar da bincike tare da daukar matakin da ya kamata.

Karkashin dokokin Uefa dai haramtaccen lamari ne samun hannun dan wasa a harkokin da suka shafi caca yayinda hukuncinsa ke kaiwa ga dakatarwa ta tsawon lokaci.

Sanarwar da Uefa ta fitar, ta sanar da kafa kwamiti na musamman don binciken lamarin.

 A makon jiya ne dai Zlatan mai shekaru 39 ya tsawaita kwantiraginsa da AC Milan bayan zura kwallaye 17 cikin wasanni 25 a wannan kaka.

Haka zalika a baya-bayan nan ne, Zlatan ya koma fagen dokawa kasarsa leda bayan ritaya shekaru 5 baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.