Isa ga babban shafi
Wasanni - Gasar Zakarun Turai

Zlatan zai rasa karawar AC Milan da Liverpool saboda rauni

Kungiyar kwallon kafa ta AC Milan ta sanar da cewa, dan wasanta na gaba Zlatan Ibrahimovich ba zai samu damar taka leda a haduwarsu da Liverpool yau Laraba ba.

Dan wasan gaba na AC Milan Zlatan Ibrahimovic yayin zura kwallo a wani wasa.
Dan wasan gaba na AC Milan Zlatan Ibrahimovic yayin zura kwallo a wani wasa. MIGUEL MEDINA AFP
Talla

Mai horar da kungiyar ta Milan Stefano Pioli a jawabinsa yayin taron manema labarai game da wasan na yau karkashin gasar cin kofin zakarun Turai, ya ce Zlatan yanzu haka na fama da jinyar rauni.

Kocin na AC Milan ya ce Zlatan ya samu rauni bayan wasansu na ranar Lahadi da ya yi nasarar zura kwallo guda wanda dama shi ne wasansa na farko bayan dogowar jinyar da ya tafi.

A cewar Kocin Zlatan wanda zai cika shekaru 40 a watan Oktoba mai zuwa, baya cikin wani yanayi da zai hana shi doka wasan amma za su hutar da shi don tunkarar wasannin gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.