Isa ga babban shafi

Qatar na duba yiwuwar sayen kungiyoyin firimiyar Ingila 3

Qatar na sanya ido kan wasu manyan kungiyoyi 3 da ke doka gasar firimiyar Ingila domin ta saye su baki daya ko kuma wani sashe na su. 

Shugaban hukumar zuba jari a bangaren wasanni, Nasser Al-Khelaifi tare da shugaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Florentino Perez.
Shugaban hukumar zuba jari a bangaren wasanni, Nasser Al-Khelaifi tare da shugaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Florentino Perez. REUTERS/Ahmed Jadallah
Talla

Daga cikin wadannan kungiyoyi har da Manchester United da Liverpool da Tottenham Hotspur, matakin da ke zuwa bayan kasar ta fuskanci caccaaka a lokacin da ta yi ta fafutukar neman daukar nauyin gasar cin kofin duniya ta 2022 da aka kammala kwana-nan nan. 

An jinjina wa Qatar kan yadda ta dauki nauyin gasar ta cin kofin duniya mafi tsada a tarihin duniya. 

Shafin Bloomberg ya rawaito cewa, tuni shugaban zuba hannayen jarin wasanni na kasar Qatar, Naseer Al-Khelaifi ya tattaunawa da shugaban kungiyar Tottenham, Daniel Levy kan yiwuwar wani hannun jari mai tsoka na kungiyar ta London. 

Kazalika Bloomberg ya ce, Qatar din na duba yiwuwar mallakar Manchester United da Liverpool baki dayansu. 

A cewar Bloomberg ta tattaro bayanan ta ne daga wani mutum da ya bukaci a sakaya sunansa, amma ya na cikin mutanen da suka halarci taron tattaunawa kan batun sayar da kungiyoyin ga Qatar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.