Isa ga babban shafi

Muhimman abubuwan da suka faru yayin gasar cin kofin Duniya a Qatar

A ranar lahadin da ta gabata ne aka kammala gasar lashe kofin duniya karo na 22 da aka gudanar a kasar Qatar wacce ita ce ta farko da aka gudanar a yankin kasashen Larabawa.

Kungiyar kwallon kafar Argentina wacce ta lashe kofin Duniya a Qatar
Kungiyar kwallon kafar Argentina wacce ta lashe kofin Duniya a Qatar AP - Martin Meissner
Talla

Tun bayan baiwa Qatar damar daukar nauyin gudanar da gasar, ake ta cece-kuce akan shirin kasar, amma daga bisa shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino ya bayyana gasar ta bana a matsayin gagara misali, musamman irin yadda Qatar ta shiryawa gasar.

Tawagar kasar Argentina ce ta samu nasarar lashe kofin gasar bayan da aka buga mintuna 120 babu kasar da ta samu nasara akan abokiyar karawarta tsakanin Argentina da Faransa.

Kasar Qatar ta taka gagarumar rawa wajen gabatar da ingantattun filayen wasannin guda 8 wadanda akayi amfani da su  wajen gudanar da wasannin wanda aka bayyana cewar mutane sama da biliyan sun kalla ta kafar talabijin.

Akwai ababe da dama da suka faru a gasar ta bana wanda za’a dade ba’a mance da su ba.

A wannan karon ne dai aka kashe kudin da ba’a taba kashewa ba wajen shirya gasar lashe kofin duniya, domin dai Qatar ta kashe kusan dala biliyan 220 wajen shirya karbar bakuncin gasar wanda ya ninka wanda Rasha ta kashe a shekarar 2018 kusan sau 16.

Har wayau, a gasar ta bane ce aka kara yawan kudin da ake baiwa zakarar da ta samu nasarar lashe gasar, domin dai a yanzu Argentina ta samu dala miliyan 42, yayin da ita kuma Faransa ta samu dala miliyan 30. A jumlace FIFA ta kashe dala miliyan 440 wajen kyautuka ga kasashen da suka halarci gasar sabanin dala miliyan 400 da aka saba kashewa.

Kuma wani abin dauke hankali, Qatar ta mika kyaututtuka ga daukacin wadanda suka halarci kowanne wasan da aka kara a cikin kwanaki 29 da aka kwashe ana fafatawa.

A cikin wasanni 64 da kasashe 32 suka buga a gasar, an samu nasarar saka kwallaye 172, wanda shine irinsa na farko a tarihin gasar da aka samu nasarar cin kwallaye da yawa a gasa guda, duk da cewar a wadda aka gudanar a shekarar 1998 da Faransa ta dauki nauyinsa da kuma ta shekarar 2014 da Brazil ta dauki nauyi anci kwallaye 171 a kowacce daga cikinsu.

Kasar Faransa da ta zo ta biyu a gasar ce tafi yawan kwallaye bayan da ta zura kwallaye 16, sai Argentina da ta lashe gasar wadda ta zura kwallaye 15.

Kasashen Belgium da Denmark da Tunisiya da Wales da kuma Qatar da ta sauki baki, sune suka zura mafi karancin kwallaye a gasar, domin dai dukkanin su jefa kwallo guda-guda a raga kafin ficewarsu daga gasar.

Haka nan a wannan karon ne mace ta fara alkalanci a gasar cin kwallon kafa ta duniya ta maza, inda Stephanie Frappart ‘yar kasar Faransa ta zamo ta farko data fara busa wasan da akayi tsakanin Jamus da Costa Rica a ranar 1 ga watan Disamba.

Salima Mukansanga ‘yar asalin kasar Rwanda ta zama mace ta farko daga nahiyar Afrika da ta yi alkalanci a gasar, abinda ke nuna cewar alkalai mata sun kama hanyar shiga a dama da su a alkalancin wannan gasar ta maza.

Alkalan wasa a gasar lashe kofin duniya ta bana, sun bada katin gargadi har sal 176, kuma Argentina ce tafi yawan samu domin tana da 17 sai Saudiya mai 14 Netherlands 13, kasashen Portugal da Brazil suka samu mafi karanci domin kowacce daga cikin su na da shida- shida.

Sai kuma katin kora guda biyar da aka nuna a gasar, ciki harda wanda aka ba mai horas da tawagar kasar Koriya ta Kudu.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Gianni Infantino tare da masu sharhi akan harkokin wasanni na ci gaba da jinjinawa kasar Qatar akan gagarumar nasarar da ta samu wajen daukar nauyin wannan gasa wanda aka kammala ta cikin kwanciyar hankali.

Ganin nasarar da aka samu, tasa Infantino ya sake bayyana aniyarsa na ganin na kara yawan kasashen da zasu dinga shiga gasar zuwa 48 domin dada inganta shi da kuma baiwa kowacce nahiya damar gabatar da karin kasashe.

Bisa dukkan alamu, duk wanda ya bibiyi yadda wadannan wasanni suka gudana, ya tabbatar da cewar Qatar ta fitarwa kasashen Larabawa da kuma nahiyar Asia kitse a wuta wajen daukar nauyin wannan gasa   ta bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.