Isa ga babban shafi

Dakin Messi a Qatar ya zama wurin ajiye kayan tarihi

Jami’ar kasar Qatar ta sanar da cewar za ta maida dakin otel din da kyaftin din Argentina Lionel Messi ya zauna a lokacin gasar lashe kofin duniya ta shekarar 2022, wani dan karamin wajen adana kayan tarihi.

Lionel Messi
Lionel Messi AP - Martin Meissner
Talla

Dakin wanda aka bayyana cewar a karshen gasar Messi da tsohon abokin wasan sa Aguero sunyi amfani dashi, daga yanzu ba za’a sake saukar baki a cikin sa ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Qatar QNA ya sanar.

Dan wasan da ya lashe kyautar lambar yabo ta Ballon d’Or sau 7, ya ta ka rawa wajen taimakawa kasar sa ta Argentina wajen lashe gasar karon farko cikin shekaru 36.

A karshen gasar dai da aka kammala a ranar 18 ga wannan watan, an bashi kyautar gwarzon dan wasa na gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.