Messi ya zama gwarzon dan wasan shekara na BBC
An bayyana kyaftin din Argentina da ya lashe kofin duniya a Qatar Lionel Messi a matsayin gwarzon dan wasan shekara na BBC a shekarar 2022.
Wallafawa ranar:
Messi, mai shekaru 35, ya jagoranci Argentina wajen lashe kofin duniyar na farko a cikin shekaru 36 a gasar da aka yi a Qatar.
Dan wasan gaban na Paris St-Germain shi ne kuma ya lashe kwallon zinare da ake bai wa dan wasa da ya fi bajinta a gasar, bayan da ya saka kwallye 7 a raga a gasar da ita ce ta 5 da ya buga a tsawon lokacin da ya shafe ya na taka leda.
An yi ittifakin cewa tsohon dan wasan na Barcelona ya na daya daga cikin gwanayen ‘yan wasan kwallon kafa a da aka taba yi a duniya.
Messi ya ci kwallaye 2 a wasan karshe da suka fafata da Faransa a wannan gasar kofin duniya din.
Dan wasan ya lashe kofin zakarun Turai 4, La Liga 10 a Barcelona, sai kofin lig din Faransa 1 a PSG inda a tsawon shekarun taka ledarsa ya ci kwallaye 793.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu