Isa ga babban shafi

Messi da Mbappe na kankankan a tseren lashe takalmin zinare

A ranar Lahadi mai zuwa za’a Karkare wasannin gasar cin kofin duniya ta 2022 a kasar Qatar, wanda masana harkokin wasannin suka yaba amatsayin wanda yayi nasara kuma mafi girma da aka taba gani, inda za’a doka wasan karshe tsakanin Faransa da Argentina.

Lionel Messi na Argentina da Kylian Mbappé na kasar Faransa
Lionel Messi na Argentina da Kylian Mbappé na kasar Faransa © AFP / ALFREDO ESTRELLA,PAUL ELLIS
Talla

Dukkan kungiyoyin biyu na neman kofin ne a karo na uku, domin samun karin tauraro a rigar wasa ko Jesi.

Wa zai lashe takalmin zinare

Sannan wannan wasa na ranar Lahadi zai fayyace wanda zai lashe kyautar takalmin zinare na yawan kwallaye tsakanin Lionel Messi, Kylian Mbappe, Olivier Giroud da Julian Alvarez.

Yanzu dai Messi da Mbappe suna da kwallaye 5/5 a raga yayin da Giroud da Alvarez ke da kwallaye 4/4 kowannensu.

Sauran 'yan wasa kamar Goncalo Ramos na Portugal, da na Spain Alvaro Morata da Marcus Rashford da Bukayo Saka na Ingila da dan wasan Ecuador Enner Valencia da Richarlison na Brazil da Cody Gakpo Netherlands duk na da kwallaye 3/3 ko kowanne da zasu iya kalubalantar masu 4/4 an riga an kore su.

Za a bayar da kyautar takalmin zinare ne ga dan wasan da ya fi cin kwallaye. Idan 'yan wasa sun hadu a daidaiton kwallaye, za’a bawa wanda ya fi taimakawa aka zura kwallo. A hakan ma idan sunyi daidai to za’a duba wanda yafi saurin cin kwallo.

Messi na kan gaba

Idan aka kammala wasa babu ci ranar Lahadi, to ana iya bayyana Messi a matsayin wanda ya yi nasara saboda sau uku ya taimaka aka zura kwallo, idan aka kwatanta da Mbappe da yayi hakan sau biyu.

Faransa ta kafa tarihi

A halin da ake ciki, Faransa ce kasa ta farko da ke rike kambin kofin duniya na FIFA da ta kai wasan karshe tun bayan wanda Brazil ta yi a shekarar 1998 kuma ta zama kasa ta biyar da ta lashe gasar cin kofin duniya ta FIFA sannan ta kai wasan karshe a jere bayan Italiya (1934-1938) da Brazil (1958 -1962), Argentina (1986-1990) sai kuma Brazil din de a (1994-1998).

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.