Isa ga babban shafi

Messi ya ce zai ci gaba da yi wa Argentina wasa

Lionel Messi  ya ce ba zai yi ritaya daga wasa kwallon kafa na kasa da kasa  ba, bayan da ya jagoranci tawagar Argentina zuwa lashe kofin duniya na farko a cikin shekaru 36.

Dan wasan Argentina,  Lionel Messi.
Dan wasan Argentina, Lionel Messi. REUTERS - KAI PFAFFENBACH
Talla

Ya yi wannan bayannin ne bayan da kasarsa ta doke Faransa 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron raga a wasan karshe na gasar kofin duniya da aka yi a Qatar, biyo bayan cajaras 3-3 da suka yi.

Messi wanda zai cika shekaru 36 a shekara mai kamawa ya yi amannnar cewa har yanzu akwai gudummawa da zai bai wa kasarsa a fannin kwallon kafa.

Dan wasan ya ce yana jin dadin kasancewa a tawagar kwallon kafar kasarsa, kuma zai  so ya ci gaba da buga mata karin wasanni.

Messi,  wanda wannan ita ce gasar kofin duniyarsa ta 5 ya ci kwallaye 2 a wasan karshen, kana ya ci 1 a lokacin bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Shine ya ci kyautar dan wasan da ya fi yin fice a gasar, bayan da ya yi bajinta ya ci kwallaye 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.