Isa ga babban shafi

Messi zai koma wasa a Inter Miami ta Amurka - rahotanni

Lionel Messi ya shirya don amincewa da komawa kungiyar kwallon kafa ta Inter Miami a kaka mai zuwa, kamar yadda majiyoyi suka shaida mana.

Lionel Messi, dan wasan Argentina da Paris Saint Germain.
Lionel Messi, dan wasan Argentina da Paris Saint Germain. © AFP - KIRILL KUDRYAVTSEV
Talla

Dan wasan gaban na Argenitina, yanzu haka yana wasa a kungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain a kwantiragin shekaru 2, wanda zai kare a shekarar 2023.

A shekarar 2021 ne ya koma kungiyar daga Barcelona, bayan da kwantiraginsa ya  kare.

A yayin da ake danganta Messi da komawa Barcelona, rahotannin baya bayan nan na nuni da cewa za shi Amurka ne don murza tamola a kungiyar kwallon kafa ta Inter Miami, kungiyar da ke mallaakin tssohon dan wasan Ingila David Becham.

Rahotannin sun ce a Qatar ne Messi zai kullaa kwantiragi da Inter Miami, amma bayan gasar cin kofin duniya.

Kwantiragin zai mayar da  Messi dan wasan da ya fi daukar albashi a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.