Isa ga babban shafi

Argentina ta ayyana yau a matsayin hutu don murnar lashe kofin Duniya

Hukumar kwallon kafar Argentina ta ce a yau Talata za ta gudanar da bikin lashe kofin duniya da tawagar kwallon kafar kasar ta yi a dandalin Obelisk da ke birnin Buenos Aires, inda aka saba gudanar da shagulgulan wasanni a kasar.

Tawagar kwallon kafar Argentina.
Tawagar kwallon kafar Argentina. REUTERS - MATIAS BAGLIETTO
Talla

Bugu da kari, gwamnatin kasar ta ayyana yau Talata a matsayin ranar hutu, inda har bankuna ba za su yi aiki ba don nuna farin cikin lashe wannan kofi mai daraja.

Hukumar kwallon kafar kasar ta ce a yau ne tawagar kwallon kafar za ta tashi zuwa wannan dandali na Obelisk don wannan biki.

Argentina ta doke Faransa da kwallaye 4-2 a bugun fenariti bayan da suka tashi wasa canjarasa 3-3 a wasan da aka sanya a cikin jerin wasannin karshe mafiya kayatarwa da aka taba bugawa a gasar kofin duniya.

An ta sowa da murna a fadin Argentina sakamakon lashe wannan kofin da tawagar kwallon kafar kasar ta yi a karon farko cikin shekaru 36.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.