Isa ga babban shafi

Argentina da Faransa na shirin kafa sabon tarihi a Qatar

Farin ciki ya karu a yau Lahadi a kusa da filin wasa na Lusail, gabanin wasa tsakanin Argentina da Faransa.Lionel Messi na Argentina da Kylian Mbappé na Faransa kowannensu yana matsawa zuwa mafarkin tauraro na uku.

Dan wasan Faransa Kylian Mbappe
Dan wasan Faransa Kylian Mbappe REUTERS - PETER CZIBORRA
Talla

Tare da ƙwararren ɗan wasan ta, Argentina na iya kashe shekaru 36 na takaici a gasar cin kofin duniya, yayinda  Mbappé ya dauki hankalin masu sharhi da dama a Argentina.

 Tarihin gasar cin kofin Duniya yana nuna fuskokin masu cin nasara, daga Mario Kempes (1978) zuwa Hugo Lloris (2018) ta hanyar Diego Maradona (1986) da Zinédine Zidane (1998).

Shekaru hudu bayan Moscow, Faransa za ta iya lashe kambi na biyu a jere, wasan da ba a taba yin irinsa ba tun bayan Brazil na Pelé, Vava da Garrincha a 1962. Fatanta ya dangana kan Mbappé, wanda ranar talata zai cika shekaru  24 a Duniya.

Indan aka yi tuni Kungiyar kwallon kafar Faransa ta isa Qatar ne cikin rudani da rashin samun sakamako mai ban sha'awa, yan wasa da dama ne suka samu raunuka. Sanu a hankali kungiyar ta Faransa ta cimma makoma mai kyautare da shawo kan matsalolin daya bayan daya tare da juriya, haɗin kai, da kuma kwarewar wadanda suka tsira daga Rasha (Olivier Giroud, Antoine Griezmann, Raphaël Varane ...).

Kyaftin Lloris ya ce "Abin da muka samu yana da karfi sosai, amma shi ne wasan karshe mafi wahala," in ji kyaftin Lloris, yana sane da cewa dole ne ku "shirya don shan wahala, don yin kokari, ku wuce duk da gajiya".

Didier Deschamps, kyaftin din tauraruwar farko a 98 kuma koci a karo na biyu a 2018 ya ce "Abokan hamayyarmu za su kasance a filin wasa, ba a tsaye ba." Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya isa birnin Doha, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Qatar QNA ya ruwaito a safiyar yau Lahadi.

Faransa ko Argentina wace kungiya a ganin ku za ta lashe wannan kofin a Qatar?

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.