Isa ga babban shafi

An yi taron alhinin mutuwar mutane 125 a filin wasan Indonesia

Daruruwan mutane ne suka taru a wani dandali dake birnin Jakarta a ranar Lahadi, domin alhinin mutuwar mutane akalla 125, da jikkatar wasu fiye da 300, yayin wani wasan kwallon kafa, sakamakon harba hayaki mai sa hawaye a cikin filin wasan da ‘yan sanda suka yi.

'Yan wasa da Jami'an kungiyar Arema FC yayin addu'o'i a wajen filin wasa na  Kanjuruhan inda 'yan kallo da dama suka rasa rayukansu sakamakon turmutsitsin da ya biyo bayan hayaki mai sa hawayen da 'yan sanda suka harbawa masu boren rashin amincewa da sakamakon wasa.
'Yan wasa da Jami'an kungiyar Arema FC yayin addu'o'i a wajen filin wasa na Kanjuruhan inda 'yan kallo da dama suka rasa rayukansu sakamakon turmutsitsin da ya biyo bayan hayaki mai sa hawayen da 'yan sanda suka harbawa masu boren rashin amincewa da sakamakon wasa. AP - Achmad Ibrahim
Talla

Makamancin gangamin nuna bacin ran ya gudana a wasu sassan na Jakarta, baya ga taron farkon da aka yi a babban dandalin dake birnin.

An dai samu turmitsitsin da ya lakume rayukan mutane fiye da 120 a Indonesia ne, yayin wasan da Persebaya Surabaya ta doke Arema FC ranar Asabar a filin wasa na Kanjuruhan, inda wasu gungun magoya baya da sakamakon bai yi wa dadi ba suka shiga fili, abinda ya sanya ‘yan sanda amfani da karfi domin tarwatsa su.

Tuni dai shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino yayi tur da aukuwar tashin hankalin na Indonesia, wanda ya bayyana a matsayin rana mai muni ga wasan kwallon kafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.