Isa ga babban shafi

Akalla mutane 31 sun mutu a turmutsitsin cocin Fatakwal dake Najeriya

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce akalla mutane 31 ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka samu raunuka sakamakon tirmitsitsin da aka samu a wata mujami’a yau da safe a Birnin Fatakwal da ke kudancin kasar.

Ana fargabar mutane da dama sun mutu a wani coci a Fatakwal
Ana fargabar mutane da dama sun mutu a wani coci a Fatakwal © newsrangers.com
Talla

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan yankin Grace Iringe-Koko ce ta tabbatar da mutuwar mutanen da adadinsu ya kai 31.

Shaidun gani da ido sun ce an samu tirmitsitsin ne a mujami’ar dake shirin raba kyautar kayan abinci ga jama’a marasa karfi yau da safe.

Bayanan sun ce tun yammacin jiya mutane suka fara isa mujami’ar domin ganin sun samu zama cikin sahun gaba na wadanda zasu fara karba, yayin da yau da karfe 6.30 na Safiya mutane suka yi ta tururuwa domin halartar taron wanda aka shirya farawa da misalin karfe 9 na safe.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar wasu masu motsa jiki da za suyi amfani da dakin taron da aka shirya yin bikin sun bude shi da misalign karfe 8, abinda ya sa wadanda suka je domin karbar tallafin abinci kutsawa cikin dakin da karfi, abinda ya haifar da tirmitsitsin da kuma rasa rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.