Isa ga babban shafi

'Yar wasan Najeriya Tobi Amusan ta sake kafa tarihi a wasan guje-guje

'Yar wasan Najeriya Tobi Amusan ta yi nasarar kare kambunta na gasar tseren mita 100 na kasashe renon Ingila wato Commonwealth, bayan da ta kai matakin farko a ranar Lahadi a filin wasa na Alexander da ke Birmingham.

A watan da ya gabata ne, Tobi Amusan ta kafa sabon tarihi a gasar cin kofin duniya.
A watan da ya gabata ne, Tobi Amusan ta kafa sabon tarihi a gasar cin kofin duniya. REUTERS - MIKE SEGAR
Talla

‘Yar wasan ta sake kafa sabon tarihi bayan da ta kammala tseren mita 100 cikin dakika 20 da sakan 30, wanda hakan ya bata damar lashe lambar zinare ga kasarta Najeriya.

Mai rike da kambun gasar ta duniya ta kawo karshen tarihin tseren dakika 16 da sakan 65 da Brigitte Foster-Hylton ta Jamaica ta kafa a Melbourne, dake kasar Australia.

Devynne Charlton daga Bahamas ce ta zo na biyu yayin da ‘yar Birtaniyya, Cindy Sember wacce ta yi bikin cikarta shekaru 28 ranar da samu nasara a wasan dab da na kusa da karshe ta samu tagulla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.