Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Kwana biyu bayan faduwata na san zan iya ci gaba da kwallo- Eriksen

Dan wasan tsakiyar Denmark Christian Eriksen ya bayyana cewa tun kwanaki 2 bayan faduwarsa a gasar Euro ya san cewa zai iya ci gaba da taka leda sabanin yadda masana ke ikirarin yiwuwar kawo karshen kwallonsa a wancan lokaci.

Dan wasan tsakiyar Denmark Christian Eriksen.
Dan wasan tsakiyar Denmark Christian Eriksen. Liselotte Sabroe Ritzau Scanpix/AFP
Talla

Eriksen mai shekaru 29 wanda ya koma Brentford da taka leda a yanzu haka bayan da Inter Milan ta kawo karshen kwantiraginsa saboda dashen na’urar taimakawa zuciya ta ICD da aka yi masa bayan faduwa ana tsaka da wasan Euro cikin watan Yuni da ya kai shi ga bugun zuciya, ya bayyana cewa baya jin wani sauyi a tare da shi da ken una yiwuwar ya rasa karsashin taka leda a fagen tamaula.

Karkashin dokokin Serie A a italiya dai ba a amince amfani da ‘yan wasan da ke da dashen na’urar ta ICD taka leda karkashin gasar ba, amma rashin irin wannan doka a Firimiyar Ingila ya sa dan wasan kulla kwantiragi da Brentford a ranar karshe ta kulle kasuwar musayar ‘yan wasan watan Janairu.

A zantawarsa da manema labarai karon farko tun bayan komawa Brentford, Eriksen ya ce lokacin da abin ya faru shi da kansa ya yi tunanin rataye takalmansa, amma kwana biyu baya, yaji cewa yana da karfin iya taka leda kamar kowanne dan kwallo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.